Showing 1-20 of 40 items.

A kan mẽ suke tambayar jũna?

A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur"ãni)?

Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?

A"aha! Zã su sani.

Kuma, a"aha! Zã su sani.

Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?

Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?

Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?

Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?

Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?

Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?

Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?

Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?

Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?

Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?

Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.

Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama"a jama"a.

Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.

Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.

Error (#32)

Error (#32)

An internal server error occurred.

The above error occurred while the Web server was processing your request.

Please contact us if you think this is a server error. Thank you.