
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa

Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?

Domin yini mai girma.

Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?

Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.

Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?

Wani 1ittãfi ne rubũtacce.

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.

Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.

Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.

A"aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.

A"aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.

Sa"an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.

Sa"an nan a ce:"Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."

A"aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã"ã yana a cikin Illiyyĩna?

Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?

Wani littãfi ne rubũtacce.