Showing 61-80 of 111 items.

Suka ce:"Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne."

Kuma ya ce wa yaransa,"Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo."

To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce:"Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan"uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne."

Ya ce:"Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan"uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."

Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce:"Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan"uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki."

Ya ce:"Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce:"Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa."

Kuma ya ce:"Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."

Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu,ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma"abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan"uwansa zuwa gare shi, ya ce:"Lalle nĩ ne ɗan"uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."

Sa"an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma"auni a cikin kãyan ɗan"uwansa sa"an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne."

Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su:"Mẽne ne kuke nẽma?"

Suka ce:"Munã nẽman ma"aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi."

Suka ce:"Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba."

Suka ce:"To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?"

Suka ce:"Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai."

To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan"uwansa. Sa"an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan"uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan"uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma"abũcin ilmi akwai wani masani.

Suka ce:"Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan"uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce:"Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa."

Suka ce:"Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa.Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa."

Ya ce:"Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan,haƙĩƙa, azzãlumai ne."

Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce:"Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."