Showing 21-40 of 111 items.

Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa,"Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu,a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al"amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."

Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce,"Yã rage a gare ka!" ya ce:"Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"

Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.

Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce:"Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."

Ya ce:"Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida:"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."

"Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya."

Sa"an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce:"Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!"

"Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure."

Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce:"Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."

Sa"an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce:"Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce:"Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã"ika ne mai daraja!"

Ta ce:"To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu."

Ya ce:"Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."

Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani.

Sa"an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci.

Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ¦ayansu ya ce:"Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce:"Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa."

Ya ce:"Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa , kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne."

"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is"hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."

"Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?"

"Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku.Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."