Showing 1-20 of 83 items.

Y. S̃.

Inã rantsuwa da Al-ƙur"ãni Mai hikima.

Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni.

A kan hanya madaidaiciya.

(Allah Ya saukar da Al-kur"ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.

Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.

Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa"an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.

Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.

Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.

Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur"ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.

Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.

Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma"abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni suka jẽ mata.

A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa"an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce:"Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku."

Suka ce:"Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi."

Suka ce:"Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku."

"Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne."

Suka ce:"Lalle mũ munã shu"umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku."

Suka ce:"Shu"umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã"a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi."

Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce:"Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan.