Showing 1-20 of 135 items.

¦. H.

Ba Mu saukar da Alƙur"ãni a gare ka dõmin ka wahala ba.

Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah.

(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka.

Mai rahama, Ya daidaita a kan Al"arshi.

Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya.

Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa.

Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau.

Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?

A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa,"Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar."

Sa"an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi,"Ya Mũsã!"

"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa."

"Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi."

"Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni."

"Lalle ne Sa"a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa."

"Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka."

"Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!"

Ya ce:"Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta."

Ya ce:"Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!"

Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa.