Showing 81-88 of 88 items.

"Zuwa ga yinin lõkaci sananne."

Ya ce,"To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya.

"Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su."

(Allah) Ya ce,"To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa."

"Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya"

Ka ce:"Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa."

"Shĩ (Alkur"ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta."

"Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa a bayan ɗan lõkaci."