Showing 61-80 of 88 items.

Suka ce:"Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã."

Kuma suka ce:"Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?"

"Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?"

Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.

Ka ce:"Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa."

"Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara."

Ka ce:"Shĩ (Alkur"ãni) babban lãbãri ne mai girma".

"Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!"

"Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama"a (malã"iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma."

"Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."

A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã"iku,"Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã.

"Sa"an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi."

Sai malã"ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.

Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.

(Allah) Ya ce,"Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?"

Ya ce,"Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã."

Ya ce,"To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la"ananne ne."

"Kuma lalle a kanka akwai la"anaTa har zuwa rãnar sakamako."

Ya ce,"Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."

Ya ce,"To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,