Showing 41-60 of 88 items.

Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce:"Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."

Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.

Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali.

Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al"amari ga Allah ne.

Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls"hãƙa da Ya"aƙũba, ma"abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra.

Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira).

Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta.

Kuma ka ambaci Isma"ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu.

Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma.

Gidãjen Aljannar zama , alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su.

Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga"ya"yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã.

Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna.

Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa"adi ga rãnar hisãbi.

Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa.

Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma.

Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita.

Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini.

Da wani daga siffarsa nau"i-nau"i.

Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne.

Suka ce:"Ã"a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar).