Showing 1-20 of 52 items.

A. L̃. R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi,Abin gõdẽwa.

Allah wanda Yake Yanã da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone yã tabbata ga kãfirai daga azãba mai tsanani.

Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah,kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa.

Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu. Sa"an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so,Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa,"Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun) Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya.

Kuma a lõkacin da Mũsã yace wa mutãnensa,"Ku tuna ni"imar Allah a kanku a lõkacin da Ya tsĩrar da ku daga mutãnen Fir"auna, sunã yi muku mummunar azãba, kuma sunã yanyanka ɗiyanku, kuma sunã rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa mai girmã daga Ubangijinku."

Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar,"Lalle ne idan kun gõde, haƙĩƙa, Inã ƙãramuku, kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta, tabbas, mai tsanani ce."

Kuma Mũsã ya ce:"Idan kun kãfirta kũ da waɗanda suke a cikin ƙasa, gabã ɗaya, to, lalle ne Allah haƙĩƙa Mawadãci ne, Mai yawan gõdiya."

Shin lãbãrin waɗanda suke a gabãninku, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa bai zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bãyansu bãbu wanda yake sanin su fãce Allah? Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji mabayyana, sai suka mayar da hannayensu a cikin bãkunansu, kuma suka ce:"Lalle ne mũ, mun kãfirta da abinda aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa munã a cikin shakkada abin do kuke kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kõkanto."

Manzanninsu suka ce"Ashe, akwai shakka a cikin (sha"anin) Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa Yanã kiran ku dõmin Ya gãfarta muku zunubanku, kuma Ya jinkirtã muku zuwa ga ajali ambatacce?" Suka ce:"Ba ku zama ba fãce mutãne misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani."

Manzanninsu suka ce musu,"Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.

"Kuma mẽne ne a gare mu, bã zã mu dõgara ga Allah ba, alhãli kuwa haƙĩƙa Yã shiryar da mu ga hanyõyinmu? Kuma lalle ne munã yin haƙuri a kan abin da kuka cũtar da mu, kuma ga Allah sai mãsu dõgaro su dõgara."

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa Manzanninsu,"Lalle ne munã fitar da ku daga ƙasarmu, kõ kuwa haƙĩƙa, kunã kõmowã acikin addininmu." Sai Ubangijinsu Ya yi wahayi zuwa gare su,"Lalle ne, Munã halakar da azzãlumai."

Kuma haƙĩƙa, Munã zaunar da ku ga ƙasa a bãyansu. Wancan ne abin gargaɗi ga wanda ya ji tsõron matsayiNa, kuma ya ji tsõron ƙyacẽwãTa.

Kuma suka yi addu"ar alfãnu. Kuma kõwane kangararre mai tsaurin kai ya tãɓe.

Daga bãyansa akwai Jahannama, kuma anã shãyar da shi daga wani ruwa, surkin jini.

Yanã kwankwaɗarsa, kuma bã ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta jẽ masa daga kõwane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bãyansa akwai azãba mai kauri.

Misãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga abin da suka yi tsirfa a kan kõme.Wancan ita ce ɓata mai nĩsa.

Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa. Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa.

Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah.