Showing 121-123 of 123 items.

kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni,"Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne.

"Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ne."

Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al"amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba.