Showing 61-80 of 85 items.

Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma"abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.

Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?

Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah.

Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa"an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana.

Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.

Ka ce:"Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu."

Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa"an nan daga maniyyi, sa"an nan daga sãren jini, sa"an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa"an nan dõmin ku isa ga cikar ƙarfinku sa"an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammãninku ko zã ku hankalta.

Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al"amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa.)

Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, yadda ake karkatar da su?

Waɗanda suka ƙaryata, game da Littãfin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani.

A lõkacin da ƙuƙumma suke a cikin wuyõyinsu, da sarƙõƙi anã jan su.

A cikin ruwan zãfi, sa"an nan a cikin wutã anã babbaka su.

Sa"an nan a ce musu,"Ina abin da kuka kasance kunã shirki da shi"

"Wanin Allah?" Suka ce:"Sun ɓace mana. Ã"a, ba mu kasance munã kiran kõme ba a gabani."Kamar wancan ne Allah Yake ɓatar da kãfirai.

Wancan dõmin abin da kuka kasance ne kunã farin ciki da shi, a cikin ƙasã, bã da hakki ba, kuma da abin da kuka kasance kunã yi na nishãɗi.

Ku shiga kofõfin Jahannama kunã madawwama a cikinta. To, mazaunin mãsu girman kai yã mũnana.

Sabõda haka ka yi haƙuri. Lalle wa"adin Allah gaskiya ne. To, kõ dai lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muka yi musu wa"adi da shi kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su.

Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu"ujiza fãce da iznin Allah. Sa"an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can.

Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci.

Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku.