Showing 41-60 of 85 items.

"Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã?"

"Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara."

"Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne"yan wutã."

"To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al"amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyinSa."

Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir"auna.

Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa"a take tsayuwa, anã cẽwa,"Ku shigar da mutãnen Fir"auna a mafi tsananin azãba."

Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni),"Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?"

Waɗanda suka kangara suka ce:"Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyinSa."

Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama,"Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana ,a yini ɗaya, daga azãba."

Suka ce:"Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce:"Na"am, sun jẽ!" Suka ce:"To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata.

Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa.

Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la"ana, kuma sunã da mũnin gida.

Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã"ĩla Littãfi.

Shiryarwa da tunãwa ga ma"abũta hankali.

Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa"adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya.

Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Lalle halittar sammai da ƙasã, ita ce mafi girma daga halittar mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni.

Lalle Sa"a, haƙĩƙa mai zuwa ce, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.

Kuma Ubangijinku ya ce:"Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu."