Showing 21-40 of 85 items.

Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah.

Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne.

Zuwa ga Fir"auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce:"Mai sihiri ne, maƙaryaci."

Sa"an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce:"Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata.

Kuma Fir"auna ya ce:"Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa. Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasã."

Kuma Mũsã ya ce:"Lalle nĩ, nã nẽmi tsari da Ubangijĩna kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda bã ya ĩmani da rãnar Hisãbi."

Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir"auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce:"Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi muku wa"adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya."

"Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana?" Fir"auna ya ce:"Bã ni nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa."

Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce:"Ya mutãnẽnã! Lallene, nĩ, inã yi muku tsõron kwatankwacin rãnar ƙungiyõyi."

"Kwatankwacin al"adar mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da waɗanda ke a bãyansu. Kuma Allah bã Ya nufin zãlunci ga bãyinSa."

"Kuma ya mutãnẽna! Lallenĩ, inã yi muku tsõron rãnar kiran jũna."

"A rãnar da zã ku jũya, kunã mãsu bãyar da bãya (gudãne) bã ku da wani mai tsaro daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa."

"Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce,"Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa." Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka."

"Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa."

Kuma Fir"auna ye ce,"Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi."

"¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir"auna mũnãnan aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir"auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra."

Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce:"Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa."

"Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata."

"Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba."