Showing 61-75 of 75 items.

Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba.

Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.

Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra.

Ka ce:"Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!"

Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka,"Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra."

Ã"aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya.

Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.

Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa"an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.

Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.

Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa.

Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama"a-jama"a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu,"Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce,"Na"am,"kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"

Aka ce,"Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa"an nan mazaunin makangara yã munana."

Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama"a-jama"a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu,"Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama( a cikinta)."

Kuma suka ce:"Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa"adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma"aikata.

Kuma kanã ganin malã"iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al"arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce,"Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu."