Showing 41-60 of 75 items.

Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa"an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba.

Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa"an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.

Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce:"Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta?"

Ka ce:"Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa"an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku."

Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki.

Ka ce:"Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa."

Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su.

Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu.

To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa"an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni"ima daga gare Mu, sai ya ce:"An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã"a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba.

Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba.

Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba.

Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni.

Ka ce: (Allah Ya ce):"Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."

"Kuma ku mayar da al"amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa"an nan kuwa bã zã a taimake ku ba."

"Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba."

"Kada wani rai ya ce:"Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah" kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!""

"Ko kuma (kada) ya ce:"Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.""

"Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba,"Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.""

"Na"am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai."

Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai?