Showing 1-20 of 49 items.

Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).

Da wani littãfi rubũtacce.

A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.

Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).

Da rufin nan da aka ɗaukaka.

Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).

Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.

Bã ta da mai tunkuɗẽwa.

Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.

Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.

To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.

Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.

(A ce musu):"Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."

"To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"

"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni"ima.

Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.

(A ce musu):"Ku ci, ku sha, da ni"ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.