Showing 41-60 of 129 items.

Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.

Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa.Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah,"Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne."

Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata.

Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.

Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa"an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo.

Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu zama.

Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai"yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,

Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al"amari, har gaskiya ta zo, kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,

Kuma daga cikinsu akwai mai cẽwa,"Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.

Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce:"Haƙĩƙa, mun riƙe al"amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki.

Ka ce:"Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara."

Ka ce:"Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."

Ka ce:"Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai."

Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.

Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha"awa, kuma haka"ya"yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.

Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.

Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga.

Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha"anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi.

Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce:"Ma"ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne."

Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.