Showing 1-8 of 8 items.

Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).

Har kuka ziyarci kaburbura.

A"aha! (Nan gaba) zã ku sani.

Sa"an nan, tabbas, zã ku sani.

Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.

Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.

Sa"an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.

Sa"an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni"imar (da aka yi muku).