Showing 1-20 of 182 items.

Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

Sa"an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.

Sa"an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.

Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.

Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.

Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama"a mafi ɗaukaka (Malã"iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.

Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.

Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.

Ka tambaye su:"Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.

Ã"a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.

Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.

Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.

Kuma su ce,"Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."

"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa,ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?

"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"

Ka ce:"Na"am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."

Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.

Kuma su ce:"Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."