Showing 1-20 of 53 items.

Ḥ. M̃.

Ĩ. Ṣ̃.

Kamar wancãn (asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka .

(Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.

Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã"iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba.

Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur"ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa"ĩr.

Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al"umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki.

Kõ kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke rãyar da matattu alhãli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kõme.

Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al"amarĩna.

(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma"aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Shĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yanã shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yanã hukuntãwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kõme.

Ya shar"anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.

Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.

Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce,"Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take."

Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al"amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani.

Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa anã) tsammãnin Sa"ar kusa take?

Waɗanda ba su yi ĩmãnida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa"a, haƙĩƙa,sunã a cikin ɓata Mai nĩsa.

Allah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi.

Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira.