Showing 1-20 of 227 items.

¦. S̃. M̃.

Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.

Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!

Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.

Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.

To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.

Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau"i mai kyau?

Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.

Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.

Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã,"Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.

"Mutãnen Fir"auna bã zã su yi taƙawa ba?"

Ya ce:"Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.

"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.

"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."

Ya ce:"Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."

"Sai ku je wa Fir"auna, sa"an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."

"Ka saki Banĩ Isrã"ila tãre da mu."

Ya ce:"Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"

"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"

Ya ce:"Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."