Showing 1-20 of 78 items.

(Allah) Mai rahama.

Yã sanar da Alƙur"ani.

Yã halitta mutum.

Yã sanar da shi bayãni (magana).

Rãnã da watã a kan lissãfi suke.

Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu"i.

Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.

Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.

Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.

Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.

A cikinta akwai"ya"yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.

Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.

To, sabõda wanne daga ni"imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?

Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.

Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.

To, sabõda wanne daga ni"imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.

To, sabõda wanne daga ni"imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.

A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.