Showing 1-20 of 64 items.

(Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa.

Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.

Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.

Kuma waɗanda ke jĩfar mãtã masu kãmun kai, sa"an nan kuma ba su jẽ da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai.

Fãce waɗanda suka tũbadaga bãyan wannan, kuma suka gyãru, to lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah,"Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta."

Kuma ta biyar cẽwa"La"anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata."

Kuma yanã tunkuɗe mata azãba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah,"Lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga maƙaryata."

Kuma tã biyar cẽwa"Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta."

Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar tũba ne, Mai hikima!

Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama"a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã"a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã"anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.

Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce:"Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?"

Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.

Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne,dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa.

A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne.

Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba,"Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma"?

Allah Yanã yi muku wa"azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai.

Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.

Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba.

Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai!