Showing 1-20 of 46 items.

Ina rantsuwa da mala"iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

Sa"an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.

Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.

Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

Sunã cẽwa"Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

Suka ce:"Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.

Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?

Ka tafi zuwa ga Fir"auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.

"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.

"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"

Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.