Showing 1-20 of 93 items.

¦.S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur"ãni ne da Littãfi mai bayyanawa.

Shiriya ce da bushãra ga mũminai.

Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ,sunã yin yaƙĩni.

Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa.

Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra.

Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ka da Alƙur"ãni daga gun Mai hikima, Masani.

A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa"Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi."

To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa,"An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu."

"Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."

"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba,"Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa."

"Sai wanda ya yi zãlunci, sa"an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."

"Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir"auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai."

To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.

Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce:"Gõdiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."

Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce:"Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna."

Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya).

Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce,"Yã kũ jama"ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."

Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce,"Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni"imarKa wadda Ka ni"imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."

Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce:"Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"