Showing 1-20 of 62 items.

Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

Ma"abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

(Malã"ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.

Ma"abũcin ƙarfi da kwarjini, sa"an nan ya daidaita.

Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.

Sa"an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.

Har ya kasance gwargwadon zirã"i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.

Sa"an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa ).

Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.

Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?

Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa .

A wurin da magaryar tuƙẽwa take.

A inda taken, nan Aljannar makoma take.

Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.

Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.

Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.

Shin, kun ga Lãta da uzza?

Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?