Showing 1-20 of 96 items.

Idan mai aukuwa ta auku.

Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.

(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.

Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.

Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.

Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.

Kuma kun kasance nau"i uku.

Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?

Da waɗanda suka tsẽre.Sũ wɗanda suka tsẽren nan,

Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.

A ckin Aljannar ni"ima.

Jama"a ne daga mutãnen farko.

Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.

(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.

Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.

Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.

Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.

Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.

Da wasu"ya"yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.