Showing 1-20 of 40 items.

Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.

Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.

Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

Na"am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

Yanã tambaya:"Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

Aka tãra rãnã da watã

Mutum zai ce a rãn nan"Ina wurin gudu?"

A"aha! bãbu mafaka.

zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur"ãni).

Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

sa"an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.

A"aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.