Showing 1-20 of 55 items.

Sã"a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.

Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce:"Sihiri ne mai dõgẽwa!"

Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al"amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.

Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.

Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.

Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.

¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.

Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa,"Wannan yini ne mai wuya!"

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce:"Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.

Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce),"Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."

Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.

Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.

Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.

Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.

Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni

To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?

Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur"ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?

Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.

Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.