Showing 1-20 of 52 items.

Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.

Kai, sabõda ni"imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.

Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.

Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.

Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.

Ga wanenku haukã take.

Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.

Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.

Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.

Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.

Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.

Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.

Mai girman kai, bãyan haka kuma la"ĩmi ( bã ya son alhẽri).

Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.

Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce:"Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."

Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.

Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.

Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.

Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, ( ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.

Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.