Showing 1-6 of 6 items.

Ka ce"Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."

"Mamallakin mutane."

"Abin bautãwar mutãne."

"Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."

"Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."

"Daga aljannu da mutane."