Showing 1-20 of 50 items.

Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.

Sa"an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.

Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.

sa"an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.

Sa"an nan da malã"iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.

Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.

Lalle ne, abin da ake yi muku wa"adi da shi tabbas mai aukuwa ne

To, idan taurãri aka shãfe haskensu.

Kuma, idan sama aka tsãge ta.

Kuma, idan duwãtsu aka nike su.

Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.

Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.

Domin rãnar rarrabẽwa .

Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?

Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.

Sa"an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?

Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.