Showing 1-20 of 56 items.

Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.

Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi

Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,

Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,

Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.

Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri

Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure

To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.

To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya

A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.

Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,

Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya

Da ɗiyã halartattu,

Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.

Sa"an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!

Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.

Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.

Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur"ãni)

Sabõda haka, aka la"ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.

Sa"an nan, aka la"ane shi kamar yadda ya ƙaddara.