Showing 1-20 of 44 items.

Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.

Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.

Daga Allah Mai matãkala.

Malã"iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.

Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.

Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.

Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.

Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.

Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.

Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.

Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,

Da matarsa da ɗan"uwansa.

Da danginsa, mãsu tattarã shi.

Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa"an nan fansar, ta tsĩrar da shi.

A"aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,

Mai twãle fãtar goshi.

Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.

Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.

Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.

Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.