Showing 1-20 of 37 items.

Ḥ. M̃.

Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake.

Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi ga mãsu ĩmãni.

Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni.

Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa"an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.

Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni?

Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi.

Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa"an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi.

Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyinMu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya).

Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã"anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.

Wannan (Alƙur"ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi.

Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde.

Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.

Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa"an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã"ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).

Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).

Sa"an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ"a ta al"amarin.Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba.

Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.

wannan (Alkur"ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.