Showing 81-99 of 99 items.

Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.

Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.

Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.

Sa"an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.

Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã"a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.

Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur"ãni mai girma.

Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau"i-nau"i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.

Kuma ka ce:"Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne."

Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,

Waɗanda suka sanya Alƙur"ãni tãtsuniyõyi.

To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.

Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.

Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.

Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa"an nan da sannu zã su sani.

Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).

Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.

Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.