Showing 61-80 of 99 items.

To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,

Ya ce:"Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."

Suka ce:"Ã"a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."

"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."

"Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."

Kuma Muka hukunta wancan al"amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.

Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.

Ya ce:"Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."

"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."

Suka ce:"Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"

Ya ce:"Ga waɗannan,"ya"yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."

Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.

Sa"an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.

Sa"an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.

Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.

Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.

Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.

Kuma lalle ne ma"abũta Al"aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!

Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.

Kuma lalle ne haƙĩƙa ma"abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.