Showing 41-60 of 99 items.

Ya ce:"Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."

"Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."

Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma"a1kawartarsu gabã ɗaya.

Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz"i daga gare su rababbe.

Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.

"Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."

Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama"yan"uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.

Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba.

Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.

Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.

Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.

A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce:"Sallama." Ya ce:"Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."

Suka ce:"Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."

Ya ce:"Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"

Suka ce:"Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."

Ya ce:"Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?"

Ya ce:"To, mẽne ne babban al"amarinku? Yã kũ manzanni!"

Suka ce:"Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."

"Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ,haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."

"Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."