Showing 21-40 of 99 items.

Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.

Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa"an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa"an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.

Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.

Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.

Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.

Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi.

Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã"iku:"Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."

"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."

Sai malã"iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.

Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.

Ya ce:"Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"

Ya ce:"Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."

Ya ce:"To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."

"Kuma lalle ne akwai la"ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."

Ya ce:"Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."

Ya ce:"To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."

"Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."

Ya ce:"Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."

"Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."