Showing 1-20 of 52 items.

Kiran gaskiya!

Mẽne ne kiran gaskiya?

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?

Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!

To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.

Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.

(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.

To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?

Kuma Fir"auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.

Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).

Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.

Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).

To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.

Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.

A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.

Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.

Kuma malã"iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã"iku) takwas na ɗauke da Al"arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.

A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.

To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa),"Ku karɓa, ku karanta littafina."

"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."