Showing 1-5 of 5 items.

Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?

Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?

Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama"a-jama"a.

Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.

Sa"an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?