Showing 1-20 of 286 items.

A. L̃. M̃.

Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.

Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.

Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.

Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.

Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu,shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba.

Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma.

Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa:"Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne.

Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni,alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa!

A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya.

Kuma idan aka ce musu:"Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce:"Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!"

To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa.

Kuma idan aka ce musu:"ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce:"Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani.

Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni,sukan ce:"Mun yi ĩmãni."Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce:"Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."

Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.

Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba.

Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.

Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa.

Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!

Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.