Showing 1-20 of 165 items.

Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske , sa"an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.

Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa"an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurinSa. Sa"an nan kuma ku kunã yin shakka.

Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa.

Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa.

Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.

Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa"an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?

Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa"an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce:"Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne."

Suka ce:"Don me ba a saukar da wani malã"ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã"ika haƙĩƙa dã an hukunta al"amarin sa"an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.

Kuma dã Mun sanya malã"ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa.

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu.

Ka ce:"Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa"an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance."

Ka ce:"Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce:"Na Allah ne." Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba."

"Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani."

Ka ce:"Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne ) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce:"Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki."

Kace:"Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina."

"Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne,( Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya."

"Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi."

"Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani."

Ka ce:"Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce:"Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur"ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa,kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce:"Bã zan yi shaidar ( haka) ba." Ka ce:"Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki."

Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.