Showing 1-20 of 73 items.

Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã"ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima.

Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa.

Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli.

Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai.

Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to,"yan"uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Annabi ne mafi cancanta ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne. Kuma ma"abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce.

Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama,kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su.

Dõmin Ya tambayi mãsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yã yi tattalin wata azãba mai raɗaɗi ga kãfirai.

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni"imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.

A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah.

A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani.

Kuma a lõkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukãtansu ke cẽwa, Allah da ManzonSa,"Ba su yi mana wa"adin kõme ba, fãce rũɗi."

Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce,"Ya mutãnen Yasriba! Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa,"Lalle gidãjenmu kuranye suke," alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu.

Kuma dã an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa"an nan aka tambaye su fitina (kãfirci), lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta (Madĩna) ba fãce kaɗan.

Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sunã yi wa Allah alkawari, a gabãnin wannan; Bã zã su jũya dõmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya.

Ka ce:"Gudun nan bã zai amfãne ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, bã zã a jĩshe ku dãɗĩ ba fãce kaɗan."

Ka ce:"Wãne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yã yi nufin wata cũta game da ku?" Kuma bã zã su sãmar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bã zã su sãmar wa kansu wani mataimaki ba.

Lalle Allah Ya san mãsu hana mutãne fita daga cikinku, da mãsu cẽwa ga"yan"uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma bã zã su shiga yãƙi ba fãce kaɗan.

Suna mãsu rõwa gare ku, sa"an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda mutuwa. Sa"an nan idan tsõron ya tafi,sai su yi muku miyãgun maganganu da harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah.

Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan.