Showing 1-11 of 11 items.

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

Sa"an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

Sai su motsar da ƙũra game da shi.

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama"ar maƙiya.

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.

Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?