Showing 1-20 of 60 items.

Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.

Sa"an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).

Sa"an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.

Sa"an nan da Malã"iku mãsu rabon al"amari (bisa umurnin Allah).

Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.

Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne

Inã rantsuwa da samã ma"abũciyar hanyõyi ( na tafiyar taurãri da sautin rediyo).

Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur"ani).

Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).

An la"ani mãsu ƙiri-faɗi.

Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.

Sunã tambaya:"Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"

Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.

(A ce musu):"Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."

Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.

Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).

Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.

Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.

Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.

Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.