Showing 1-20 of 42 items.

Yã game huska kuma ya jũya bãya.

Sabõda makãho yã je masa.

To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.

Sa"an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

Kai kuma kã shagala ga barinsa!

A"aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).

(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

A cikin hannãyen mala"iku marubũta.

Mãsu daraja, mãsu ɗã"a ga Allah.

An la"ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa"an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

Sa"an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.